Muhawarar jihar Kano: Abubuwa biyar da suka sa Kano ta shahara

Muhawarar jihar Kano: Abubuwa biyar da suka sa Kano ta shahara

 

Muhawarar jihar Kano: Abubuwa biyar da suka sa Kano ta shahara

  • Fauziyya Kabir Tukur
  • BBC Hausa, Abuja
Muhawarar jihar Kano: Abubuwa biyar da suka sa Kano ta shahara

Jihar Kano na arewa maso yammacin Najeriya ne, kuma ta zama jiha ne a ranar 27 ga watan Mayun 1967.

Ta yi iyaka da Katsina daga arewa maso yamma, ta yi iyaka da Jigawa daga arewa maso gabas, ta yi iyaka da Bauchi daga kudu maso gabas.

Tana da fadin kasa kilomita 23,131, kuma ita ce jihar da tafi kowacce yawan kananan hukumomi inda take da 44.

Mafi yawan al’ummar jihar Hausawa ne, sai kuma Fulani da sauransu.

Wata sabuwar doguwar gada da ake dab da budewa a birnin Kano
Bayanan hoto,Wata sabuwar doguwar gada da ake dab da budewa a birnin Kano

Jihar na da manyan cibiyoyin ilimi na gwamnatin jiha da na tarayya.

Baya ga wadannan abubuwa kuma, akwai wasu kebabbun abubuwa biyar da jihar ta shahara da su, kuma mun yi nazarinsu a wannan makala.

Yawan al’umma

Kano ce jihar da tafi duk jihohin Najeriya yawan al’umma.

Kidayar da aka yi a shekarar 2006 ta nuna cewa akwai mutum miliyan tara da dubu dari hudu da dari biyu da tamanin da takwas, 9,401,288.

Sannan kiyasin da aka yi a shekarar 2011 ya nuna cewa kasar na da yawan al’umma miliyan goma sha daya da dubu hamsin da takwas da dari uku, 11,058,300.

Kasuwanci

Jihar Kano ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya. Ta shahara a fannin kasuwanci tun karni na 16.

Gwamnatin jihar ta ce ana mu’amala ta naira biliyan 20 a kowacce rana a jihar a harkokin kasuwanci.

Sayar da waya da gyaranta sun zama babbar sana'a ga dubban mutane musamman matasa
Bayanan hoto,Sayar da waya da gyaranta sun zama babbar sana’a ga dubban mutane musamman matasa a jihar

Ita ce ta biyu wajen manyan masana’antu a Najeriya bayan Lagos, sai dai a baya-bayan nan rashin wutar lantarki ya jawo durkushewar bangaren masana’antu a jihar.

Jihar Kano na da manyan kasuwanni da ake hada-hadar kasuwanci daban-daban a ciki.

Akwai kasuwar Kurmi wacce tarihi ya nuna cewa an kafa ta ne tun karni na 15 kuma har yanzu tana nan a cikin birnin.

Sai kasuwar Kwari wacce ita ce kasuwar sayar da tufafi mafi girma a yankin yammacin Afirka.

Daya daga cikin kasuwanni Kano da suka dade ita ce kasuwar Dawanau, wacce ita ce kasuwar abinci mafi girma a yankin yammacin Afirka.

Sai kasuwar Sabon Gari wacce ita ma babar kasuwa ce a jihar Kano.

Tarihi

Kano gari ne mai dimbin tarihi saboda dadewarsa da kuma irin rawar da ya taka a kasuwanci da addini da ma wasu fannonin ci gaban arewacin Najeriya.

Ga wasu daga cikin manyan abubuwan tarihi da ke jihar Kano:

Masu busa kakaki da masu algaita a wajen fadar Sarkin Kano, yayin da ake zaman fadanci

Bayanan hoto,Masu busa kakaki da masu algaita a wajen fadar Sarkin Kano, yayin da ake zaman fadanci

Gidan Makama: Wannan wani gida ne na gargajiya a jihar Kano wanda aka yi shi da fasalin gine-ginen zamanin da.

Ana dai tunanin an kai shekara 500 da gina gidan Makama, wanda kuma tarihi ya nuna cewa nan ne gidan sarkin Kano a wancan zamanin.

A yanzu, an mayar da gidan wajen adana kayan tarihi na jihar.

Dutsen Dala da Goron Dutse: Wadannan duwatsu biyu dai sun zamo wasu mayan alamun jihar inda har a kan yi wa garin Kano kirari da ‘Mai Dala da Goron Dutse’.

Sannan akwai karin magana da ake cewa ‘Hangen Dala ba shiga birni ba’.

Sai dai babu wanda ya san asalin wadannan duwatsu.

Shi dai dutsen Dala, manazarta tarihi sun yi ikirarin cewa a kansa ne al’ummar Kano na wancan lokacin suke hawa su bauta wa wata aljana mai suna Tsumburbura.

Gurasa:

Tana daya daga cikin abincin da al’ummar Kano suka yi fice da ita.

Ita dai gurasa nau’i ce ta burodi wacce ta samo asali daga kasashen Larabawa na arewacin Afirka.

A karni na 8 ne aka fara cinikayya ta hanyar hamada daga kasashen arewacin Afirka, inda ‘yan kasuwa daga wannan yankin ke zuwa kasuwanci kasashen yamma da sahara.

Su kan zo da abincin da suka saba ci, ciki har da gurasa.

Ana yin gurasa da fulawa da ruwa da sukari da gishiri da yis.

Ana gasa ta a cikin manyan tukwanen kasa da ake kira tanderu.

Wannan abincin ya zama sana’a ga dubban mutane a Kano kuma akwai iyalai da dama da suka dogara da sana’ar kwabawa, gasawa da kuma siyar da gurasa.

Kannywood

Kasar Hausa ta dade da al’adun baka kamar wasanni da tatsuniya da wake-wake da gada da dai sauransu.

Sai dai zamani kan zo da sauye-sauye da kuma ci gaba a bangarori da dama na al’ada.

Irin wannan ci gaba ne al’adar Hausa ta samu a bangaren wasanni da kirkirar wasannin kwakwayo inda aka kafa masana’antar wasan Hausa ta Kannywood.

Hadiza Gabon

An kirkiri wannan masana’antar sama da shekara 20 da suka wuce, kuma ta zamo wani bangare da ke samar da kudaden shiga ga jihar Kano.

Haka kuma, matasa da dama, ba ma a jihar Kano kawai ba, har da sauran jihohin arewacin Najeriya, sun samu ayyukan yi da dama a masana’antar ta Kannywood.

Masana’anta ce mai girman gaske kuma ta samu karbuwa a fadin duniya.

Wasannin kwaikwayon Kannywood na ilmantarwa da harshen Hausa tare kuma da bunkasa al’adun Hausa.

Kammalawa

A iya cewa dai jihar Kano ta zama uwa kuma jagora ga sauran jihohin arewacin kasar ta fannin wasu abubuwan.

Sai dai har yanzu hukumomi na fafutukar ganin yadda za a shawo kan dumbin matsalolin da take fuskanta, musamman ta fuskar yawan al’umma da ke kara shiga jihar.

Amma duk da dumbin matsalolin nata, har yanzu ana ganinta a matsayin ”Ko da me ka zo an fi ka”.

 

Leave A Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Cart
Your cart is currently empty.