Ya kamata mu rage kasuwanci da kasashen Turai — Dangote

Ya kamata mu rage kasuwanci da kasashen Turai — Dangote

Aliko Dangote ya ce ya kamata kamfanonin kasashen Afirka su rinka bunkasa kasuwanci a tsakaninsu

Manyan shugabannin kamfanoni da ‘yan kasuwa a Afirka, sun gudanar da babban taro tare da wasu tsofaffin shugabannin kasashen nahiyar a birnin Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Taron ya zo da zimmar kafa kungiya mai karfi wacce za ta bunkasa harkokin kasuwanci a Afirka, a maimakon dogaro da kasashen ketare.

‘Yan kasuwar sun ce ana shigo da akasarin kayayyaki ne daga kasashen Turai da China, abin da ke kawo tarnaki ga bunkasar kasuwanci a nahiyar Afirka.

Dangote wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce ya dace manyan kamfanoni Afirka su hada kai da gwamnatocinsu ta yadda za a samar da ayyukan yi.

Ya ci gaba da cewa: “Hakan zai kawo karfafa kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka, maimakon dogaro da nahiyar Turai”.

Har ila yau, ya ce kasuwancin da ake yi a tsakanin kamfanonin Afirka bai wuce kaso 18 cikin 100 ba, don haka akwai bukatar karfafa kasuwanci a tsakanin manyan kamfanonin Afirkan.

To sai dai ya ce idan har ana so a cimma wannan bukata, to dole ne kamfanonin su rinka yin kaya masu inganci.

Karanta wadansu karin labarai masu kayatarwa

www.bbc.com/hausa https://www.bbc.com/hausa/41625829

Leave A Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Cart
Your cart is currently empty.